Kasar Sin ta yi Allah-wadai da hare-haren ta'addancin da suka yi sanadiyar rayukan mutane a kalla 37 a birnin Ankara, fadar mulkin kasar Turkiya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan yau yayin taron manema labarai, ya ce, kasar Sin ba ta goyon bayan duk wani nau'i na ta'addanci. Tana kuma fatan dukkan kasashe za su karfafa hadin gwiwa don ganin an yaki ayyukan ta'addanci.
Bugu da kari, kasar Sin tana mika ta'aziya da kuma jaje ga iyalan wadanda wadannan hare-hare suka rutsa da su.
Ministan lafiya na kasar Turkiya ya bayyana cewa, a kalla mutane 37 ne suka mutu kana wasu 125 suka jikkata ciki har da mutane 19 da suka ji munanan raunuka a harin ta'addancin da ya rutsa da birnin na Ankara a jiya Lahadi, wanda shi ne hari na biyu da aka kaddamar a cikin kasa da wata guda.(Ibrahim)