Kamfanin dillancin labarai na Faransa watau AFP ya ba da rahoto cewa, an zartas da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 13 na kasar Sin da kuma dokar jin kai a yayin zaman taro na hudu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC na 12. Haka kuma, bisa shirin din da aka tsara, ya zuwa shekarar 2020, ma'aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin zai karu daga kudin Sin RMB biliyan 67700 na shekarar 2015 zuwa RMB biliyan 92700.
Bugu da kari, kamfanin dillancin labarai na Associated Press na kasar Amurka ya fidda rahoton cewa, shugabannin kasar Sin sun sha jaddada muhimmancin kiyaye ci gaban tattalin arziki a kasar, haka kuma, ana sa ran farfadowar kasuwannin kasar sakamakon wasu matakai da gwamnatin kasar Sin ta bullo da su. (Maryam)