in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Moriyar bai daya da ke tsakanin Sin da Amurka na karuwa, in ji Li Keqiang
2016-03-16 12:41:17 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce, a shekarar bara, kasar Sin ta zama abokiyar kasar Amurka mafi girma ta fuskar harkokin ciniki, inda jimillar kasuwancinsu ta kai na dalar Amurka biliyan 560, lamarin da ya shaida cewa, moriyar bai daya da ke tsakanin kasashen 2 na karuwa, wadda kuma ta fi sabanin da ke kasancewa tsakaninsu.

Li Keqiang ya fadi haka ne a yau Laraba, yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru na gida da na wajen kasar Sin bayan an kammala taro karo na hudu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC na 12. Ya kara da cewa, zurfafa hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Amurka na amfanar kasashen biyu, har ma ga kasashen duniya baki daya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China