in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na da karfin gwiwa game da makomar tattalin arzikinta, in ji firaministan kasar
2016-03-16 12:32:01 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya fada a yau Laraba a nan Beijing cewar, kasar Sin na da karfin gwiwa game da bunkasuwar tattalin arzikinta cikin dogon lokaci.

Li Keqiang ya fadi haka ne, yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru na cikin gida da na waje, bayan kammala taro karo na hudu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC karo na 12. Ya kuma nuna cewa, kasar Sin na fuskantar matsaloli game da raya tattalin arziki, amma duk da haka, kyakkyawan fatan da kasar ke da shi na yiwuwar samun bunkasuwar tattalin arzikin ya fi matsalar da take iya fuskanta.

Li Keqiang ya kara da cewa, muddin kasar Sin ta ci gaba da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare, tattalin arzikinta ba zai samu koma baya ba, sannan daukar wannan mataki zai tabbatar da samun karin cinikayya, sannan jama'ar kasar su kyautata kwarewar kirkire-kirkire. Bugu da kari, aiki tukuru da mutanen kasar Sin ke gudanarwa, da kuma hikimarsu za su taimaka wajen ci gaba da raya tattalin arzikin Sin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China