in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin kudin kasar Sin suna iya tinkarar kalubale, in ji firaministan kasar
2016-03-16 12:34:42 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a yau Laraba a birnin Beijing cewa, hukumomin kudin kasar Sin suna iya tinkarar kalubale, kasancewar adadin kudaden da bankunan kasuwanci na kasar Sin suka adana kan bashin da suka iya bayar ya kai sama da kashi 13 cikin 100, adadin ya zarta na sauran kasashe. Haka kuma, adadin kudin da aka ajiye domin tinkarar matsalolin rancen kudi ya kai kashi 180 bisa dari, wanda ya fi adadin da gwamnatin Sin ta kayyade wato kashi 150 bisa dari. Kaza lika, ana iya yin amfani da hanyoyin kasuwanci domin rage adadin rancen kudin da kamfanonin kasar suke rike.

Bayan da aka rufe taron karo na hudu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC na 12, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da 'yan jaridun kasar Sin da na ketare, inda ya amsa tambayoyin da suka yi. A yayin da yake tsokaci kan harkokin kasuwanci da al'amuran kudi, Li Keqiang ya ce, ya kamata a ci gaba da raya tattalin arziki a bangare ba na hada-hadar kudi ba. A cewar firaministan kasar Sin, koma bayan tattalin arziki a wannan bangare zai iya haifar da babbar barazana ga harkar hada-hadar kudi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China