An yi cikakken zama karo na 4 a taron shekara shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa wato CPPCC da yammacin jiya Asabar, a babban dakin taron jama'ar kasar Sin. Inda 'yan majalissar 15 suka gabatar da jawabi game da harkokin siyasa, da aikin ba da shawara kan harkokin siyasa.
Zaunannen memba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban majalisar CPPCC Yu Zhengsheng ya halarci wannan taro.
A jawabin sa, dan majalissa Li Yuguang ya bayyana cewa, aikin kiyaye ikon mallakar fasaha na da nasaba sosai da bunkasuwar kamfannoni, ya kuma bada shawarar cewa ya kamata, a tabbatar da zurfafa yin gyare-gyare kan ikon mallakar fasaha, da karfafa kare wannan iko domin ba da kwarin gwiwa ga kirkiro sabbin kayayyaki.
A madadin 'yan majalisa 4, Zhang Shiping ta bayyana cewa, kasar Sin na fuskantar kalubale mai tsanani a fannin yawan tsofaffi, don haka ya kamata a tinkari wannan batu, da tsara manufofi domin rage mummunan tasiri da wannan batu ka iya haifawa. Ta ce kamata ya yi a maida aikin daidaita batun tsofaffi a matsayin shirin bunkasuwar kasar, da kafa manyan ayyukan more rayuwa ga tsofaffi.
Ban da haka kuma, dan majalissa Nurlan ya bayyana cewa, ya kamata a hana yaduwar tsirarun ra'ayoyin addinai, da yaki da laifukan ta'addanci da tarzoma cikin hadin kai a dukkanin fadin kasar. (Lami)