Gobe Laraba, za a rufe zaman taro na 4 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12 a babban dakin taron jama'ar kasar Sin, inda za a gabatar da rahoton gwamnati da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 13 da rahoto game da sakamakon neman samun bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma na shekarar 2015 da shirin da aka tsara na shekarar 2016, da yawan kudin da aka kashe wajen gudanar da harkokin gwamnati da kuma shirin yadda za a kashe kudade a shekarar 2016, da rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da rahoton aiki na kotun koli, da kuma rahoton aiki na babbar hukumar gabatar da kararraki da dai sauransu.
Bayan rufe wannan taro, ana sa ran firaministan kasar Sin Li Keqiang zai gana da manema labaru na gida da na waje a dakin taron jama'ar kasar Sin domin amsa tambayoyinsu.(Lami)