Kungiyar tarrayar kasashen Afrika ta AU ta kira wani taro a ranar Litinin a birnin Addis Ababan kasar Habasha, inda aka tattara kudi har dala miliyan 250, domin taimakawa kasashen hudu dake makwaftaka da tabkin Chadi ci gaba da yakin da suke da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram.
Daga kudaden, Najeriya ta samar da kudi har dala miliyan 110 adadin da ya zamo mafi yawa. Sai kuma kungiyar EU wadda ta samar da kudi dala miliyan 54.5, sauran kasashen da suka samar da kudin sun hada da Birtaniya, da Switzerland da kungiyar bai daya ta kasashen dake yankin kudu da hamadar Sahara.
A yayin taron, shugaban kasar Chadi wanda ke rike da shugabancin karba-karba na AU Idriss Deby, ya bayyana cewa, yana fatan kasashen za su cika alkawarin da suka dauka na samar da kudi ba tare da bata lokaci ba, ta yadda za a cimma nasarar dakile ta'addanci.
Kungiyar Boko Haram dai ta fara kaddamar da hare-hare a Najeriya ne tun daga shekarar 2009. A shekarun baya bayan nan kuma, kungiyar ta fara kutsawa yankunan dake kewaye da tabkin Chad, wanda hakan ya sanya kasashen yankin nuna goyon bayan su ga yakin da ake yi da Boko Haram.
Kasashen Najeriya, da Kamaru, da Chadi da Nijar sun kafa wata runduna ta hadin kai da ta kunshi sojoji 8700 a watan Fabrairun shekarar 2015, don tinkarar matsalar kungiyar Boko Haram. (Amina)