in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nijeriya na son yin shawarwari da Boko Haram
2015-12-26 13:45:10 cri
A Jiya Jumma'a 25 ga wata, shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana a babban birnin kasar, Abuja cewa, gwamnatin kasar tana son yin shawarwarin sulhu da kungiyar Boko Haram.

A yayin liyafar Kirsimati da aka yi a fadar shugaban kasa, Shuguba Buhari ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, gwamnati tana son yin shawarwari da kungiyar Boko Haram, idan kungiyar ita ma tana da ra'ayin yin hakan , haka kuma, gwamnati za ta dauki matakai da dama domin shimfida zaman lafiya a kasar.

Bugu da kari, shugaba Buhari ya ce, al'ummomin kasar Nijeriya suna samun albarkatu da dama daga kasa, kamar ma'adinai da sauransu, amma ana kuma gamuwa da kalubaloli da dama, a halin yanzu, gwamnatin na dukufa wajen warware matsalolin tsaro, neman ayyukan yi da kuma yaki da cin hanci da karbar rashawa da dai sauransu. Amma shugaba Buhari bai yi karin bayani kan shawarwarin din ba.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai Muhammadu Buhari ya sanar da cewa, an riga an cimma nasarar yaki da kungiyar Boko Haram a wasu fannoni, a halin yanzu, kungiyar ba za ta iya aiwatar da wani babban hari a kasar ba, kawai ana da wasu mambobinta ne a wasu yankunan jihar Borno na kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China