Kakakin sojin na ayyukan musamman akan harin ta'addanci Kanar Mustapha Anka ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da aka fitar ma manema labarai a Maiduguri.
A karkashin shirin za'a nade ababen fashewa a cikin itace a ajiye su a inda mutane su kan taru da wassu wurare masu muhimmanci a Maiduguri da kewaye don kawo tashin hankali, inji Anka.
A cewar shi 'yan ta'addan sun kuma gano wata dabara ta jan hankalin jama'a kawai wanda zasu dinga ihun kiran sunan Boko Baram don kawai jama'a su firgita da shi ga rudani.
Kanar Anka daga nan sai ya tunatar da jama'a cewa su kara yin taka tsantsan a lokutan bukukuwa da musamman na sabuwar shekarar nan sannan kuma har yanzu dokar hana wasan wuta na aiki ba'a dage shi ba.
A wani gefen kuma gwamnatin jihar ta Borno ta sanar da hana zirga zirgan ababen hawa a lokacin bikin sabuwar shekara da ya fada a ranar jumma'a nan.