Mista Edwards ya ce, a ganin tawagarsa dake Nijar, ana cikin yanayi mai tsanani a wurin, ana fuskantar matsalar karancin matsuguni da kuma kayayyakin da ba na abinci ba domin wadannan 'yan gudun hijira, kuma kauyuka kimanin 170 suka ga al'ummarsu ta fice a yankin Diffa na kasar Nijar.
Jami'in ya kara da cewa, HCR tana nan ta shirya kayayyakin da take da su domin amsa bukatun gaggawa tare da yin kira ga neman wani karin taimako daga abokan huldarta domin taimakawa wadannan al'ummomin.
A cewar kakakin, ana bukatar wani taimakon gaggawa kuma HCR ta gabatar da wani babban aikin rajista daga dukkan fannoni domin tantance bukatun 'yan gudun hijira cikin sauki.
A cewar wasu alkaluma na MDD, tun daga shekarar 2013, rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya ya tilastawa mutane fiye da dubu 220,300 neman mafaka a kasashe makwabta, inda 138,300 a Nijar, dubu 61 a Kamaru kana 14.100 a kasar Chadi. (Maman Ada)