in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin kunar bakin wake ya halaka mutane a kalla 4 a kasar Kamaru
2016-01-18 19:19:46 cri
Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa, wani harin bam din kunar wake da aka kai a yankin arewa mai nisa na kasar ya hallaka a kalla mutane hudu.

Shaidun gani da ido sun tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ta wayar tarho cewa, an kai harin ne a kauyen Ngue Tchewe da ke kan iyaka da Najeriya da misalin karfe 5 na safiyar yau Litinin agogon wurin..

Bayani na cewa, wani yaro ne ya tayar da bam din da ke jikinsa a cikin wani masallacin kauyen, inda ya hallaka kansa da kuma wasu mutane a kalla 4.

Ana zargin mayakan Boko Haram da kai harin, inda daga shekarar 2013 zuwa wannan lokaci, kungiyar ta hallaka mutane a kalla 1200 a yankin arewa mai nisa na kasar ta Kamaru. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China