Kamar yadda kwamandan ayyuka na yankin arewa maso gabashin kasar Manjo Janar Hassan Umoru ya sanar ma manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar Borno a ranar asabar din nan,ya ce har ila yau an samu kwato makamai na zamani masu yawan gaske daga wajen 'yan kungiyar.
Manjo Umoru ya yi bayanin cewa an kubutar da mutane 370 wadanda aka yi garkuwa da su sannan aka kai su sansanonin 'yan gudun hijira dake garin Dikwa. An lalata bindigogi 3, babur 41 duka bayan kwato su a wajen 'yan kungiyar.
Har ila yau kwamandan ya tabbatar da cewa sojoji sun yi garambawul a maboyar 'yan kungiyar dake Wala, Tirkopytir da Durubajuwe a garin Gwoza. Sannan an dakile wani shirin kai harin kunar bakin wake har guda 3 a wajen tsakanin Maiduguri zuwa Mafa duk dai a jihar ta Borno inda jami'an tsaro ke binciken masu wucewa.
Daga nan sai babban jami'in sojan yayi kira ga jami'an tsaro da sauran al'umma da su kara sa ido da kuma lura da yanayin tsaro a duk inda suke mussaman a wuraren da ake binciken ababen hawa da masu wucewa a kasa, wuraren ibada, kasuwanni , tashar mota da kuma makarantu.