Koda a makon da ya gabata shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana cewa, dakarun kasar sun karya lagon kungiyar. Wannan ya sa kungiyar ta canja salon hare-haren da ta ke kaddamarwa, ta hanyar amfani da abubuwan fashewa.
Shugaba Buhari ya ce, yanzu haka dakarun kasar sun yi nasarar kwato yankuna da dama a yankin arewa maso gabashin kasar wadanda a baya suka fada hannun mayakan na Boko Haram. Har ila, al'amura sun fara daidaita a yankin, har ma dalibai sun fara komawa makarantunsu, sannan an fara gyara gidaje da kasuwanni da aka kona, kusan za a ce yanzu harkokin sun fara komawa kamar yadda suke a baya.
Shi ma babban hafsan tsaron Najeriya janar Gabreil Olonishakin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, an samu nasara a yakin da dakarun kasar ta Najeriya ke yi da mayakan Boko Haram duk da cewa, ba za a rasa wasu 'yan koma baya nan da can ba.
Sai dai duk da wadannan nasarori da ake samu kan mayakan Boko Haram a kalla mutane 70 sun gamu da ajalinsu a wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da mayakan Boko Haram suka kaddamar a sassan kasar a ranar 25 ga watan Disamba, baya ga sama da mutane 2,000 da 'yan Boko Haram din suka halaka a cikin watanni 6 da suka gabata.
Don haka,akwai fargaban cewa, kungiyar tana kara karfi, ganin irin jerin munanan hare-haren da ta ke kaddamarwa a Abuja, fadar mulkin Najeriya zuwa kasashen Chadi da Kamaru da Nijar, da kuma yadda ta ke kara sace mutane, gami da kai hare-hare kan sansanonin soja.
A cewar Mr Adeyinka Aromolo mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, tun bayan da kungiyar ta yi mubaya'a ga kungiyar ISIL a watan Maris din wannan shekara har ta ayyana kanta a matsayin reshen kungiyar ta ISIL a yammacin Afirka, kungiyar ta ke amfani da kafofin sada zumunta na zamani wajen yada manufofinta na tayar da hankali tare da zafafa irin hare-haren da ta ke kaiwa kan fararen hula.
Ya ce, tun da ta'addaci, batu ne da ya shafi duniya baki daya, kamata ya yi Najeriya ta kara neman taimako ta fuskar soja, da makamai da kuma bayanan asiri, ta yadda za ta toshe dukkan kafofin da suke taimakawa ci gaban kungiyar.
Adeyinka ya kara da cewa, akwai bukatar da Najeriya ta samu tsarin sanya ido da tattara bayanai na zamani, wadannan su ne muhimman matakan da za su taimakawa gwamnatin a kokarin da ta ke na magance batutuwan da suka shafi jin dadin jama'a da ci gaban tattalin arziki.
Koda a baya-bayan sai da shugaba Buhari na Najerriya ya bayyana cewa, Najeriya za ta ci gaba da neman taimako daga kasashen da ke makwabtaka da ita don ganin an shawo kan matsalar ta Boko Haram, ganin cewa,matsala guda suke fuskanta.
Bugu da kari, kasar ta Najeriya za ta bukaci taimakon sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa, wajen tsugunar da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu da kuma sake gina yankunan da wannan tashin hankali ya daidaita.(Ibrahim)