An dai hallaka 'yan kasuwar ne a kauyen Jawu mai nisan kilomita 20 daga birnin Maiduguri fadar mulkin jihar ta Borno. Wani mazaunin yankin ya ce wasu matasa ne suka gano gawawwakin mutanen, bayan gudanar da binciken kwakwaf.
Kafin hakan an ce 'yan kasuwar su 13 sun yi wata tafiyar kasuwanci ne zuwa yankin na Jawu, a kuma wurin ne wasu mahara suka yi musu kwantan bauna, lamarin da ya sanya 5 daga cikin su yin batan dabo.
Mahukuntan Najeriya dai na bayyana cewa sun ci lagon kungiyar Boko Haram, wadda ta fara kaddamar da hare-hare musamman a yankunan arewa maso gabashin kasar tun a shekarar 2009.
Ko da a ranar Laraba ma sai da mayakan kungiyar suka kaddamar da hare-hare a kauyen Chibok dake jihar Borno, lamarin da ya sabbaba kisan a kalla mutane 13 tare da jikkata wasu mutanen 30. (Saminu Alhassan)