A cewar wadanda suka ganewa idanun su wannan balahira, maharan mata ne da ake zaton magoya bayan kungiyar Boko Haram ne, sun kuma yi nufin kaddamar da harin ne kan fararen hula, sai dai a lokacin da mazauna kauyen suka gano su sai suka arce, sakamakon hakan ne kuma ya sabbaba tashin bama-baman da ke jikin su.
A daya hannun kuma, wata majiyar sojojin kasar ta Kamaru, ta ce wata 'yar kunar bakin waken na daban ta tarwatsa kan ta, tare da jikkata wasu mutum biyu a ranar Lahadin karshen makon jiya, yayin da Bam din dake jikin ta ya fashe a Tolkomari dake yanki na arewa mai nisa, mai makwaftaka da iyakar kasar da Najeriya.