Harin da aka kaddamar dai wani yaro ne matashi ya aiwatar da shi bayan da ya saka bam din a cikin singiletin dake jikin shi a babbar kasauwar ta garin Gombi wanda hakan yasa yawancin wadanda harin ya rutsa dasu masu wucewa dake kusa da shi, inji wani da ya shaida da idanun shi Malam Ismail Gambo.
Mazauna garin dai sun dora alhakin wannan harin akan kungiyar boko haram masu tsatsauran ra'ayi da ikirarin zasu kafa daular musulunci a kundin tsarin mulkin kasar.
A baya ma dai, garin Gombi ya taba fuskantar harin wannan kungiyar bayan da suke ta kokarin kwace garin bayan da sojoji suka kwato shi a hannun su amma hakan ya faskara