Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau yayin taron manema labaran da aka saba yi cewa, kasar Sin ta yi allah wadai da harin da aka kai kan masu Ibadan, kuma ta yi kira ga Falesdinu da Isra'ila da su kai zuciya nesa, kana su guji daukar duk wasu matakan da za su haddasa karin tashin hankali a yankin.
Kana hanya guda da tabbatar da zaman lafiya ita ce yin shawarwarin da za ta kai ga warware sabanin dake tsakaninsu, ci gaba da kai hare-haren a tsakaninsu ba su taimaka wajen warware matsalar da suke fuskanta a halin yanzu ba, sai dai su haddasa karin matsaloli a tsakaninsu, don haka kasar Sin na fatan bangarorin biyu za su iya farfado da shawarwarin zaman lafiya a tsakaninsu cikin sauri. (Maryam)