Manufar wannan taro, ita ce tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi nahiyar ta Afirka baki daya. Ana kuma saran taron ya nazarci rahotannin ayyukan kananan kwamitocin kungiyar, da sauran shawarwari da aka cimma a tarukan baya.
A jawabinta na bude taron shugabar hukumar zartaswar kungiyar AU uwar gida Nkosazana Dlamini Zuma, ta jaddada bukatar da akwai ta ci gaba da kara kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da bunkasa al'adu da tsarin demokiradiya a nahiyar Afirka.
Ana kuma saran zabar sabon shugaban kungiyar na shekara 2016 yayin taron kolin shugabannin kungiyar, wanda zai maye gurbin shugaban kungiyar na 2015 wato Robert Mugabe na Zimbabwe.(Ibrahim)