A game da hakan, shugaban tawagar Sin a kungiyar AU na farko, mista Kuang Weilin ya bayyana cewa, tawagar za ta kara kokarin sa kaimi ga tabbatar da sakamakon da aka samu a taron kolin Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, ta yadda za ta kara ba da gudummawa ga raya dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka.
Tawagar Sin a kungiyar AU ta fara aiki ne a watan Maris na bara a hukunce kamar yadda Mista Kuang ya gaya wa wakilinmu, kafa wannan tawaga na da ma'ana sosai, wadda ta bayyana cewa, dangantaka tsakanin Sin da nahiyar Afirka, da dangantaka tsakanin Sin da kungiyar AU, dukkansu sun shiga wani sabon mataki.
Ban da haka, mista Kuang ya jaddada cewa, wannan ne karo na farko da aka kira taron kolin kungiyar AU bayan taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka shirya a Johannesburg a watan Disamban bara. Shugaban kasar Sin Xi Jinping a jawabinsa a gun taron kolin Johannesburg, ya fitar da manyan ginshikai biyar da shirye shirye 10 na yin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Hakan ya nuna alkibla ga bunkasuwar dangantaka tsakanin Sin da nahiyar Afirka, da kuma bunkasuwar dangantaka tsakanin Sin da kungiyar AU baki daya.(Fatima)