A yayin ganawar, Zhang Ming ya bayyana cewa, an raya dangantakar dake tsakanin Sin da kungiyar AU a shekarar 2015. A yayin taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a birnin Johannesburg a watan Disamba na shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin kungiyar AU Dlamini-Zuma, inda suka tabbatar da makomar dangantakar dake tsakanin Sin da kungiyar AU, da samar da gudummawa don raya dangantakar dake tsakaninsu. Kasar Sin za ta yi amfani da sakamakon taron koli na Johannesburg don aiwatar da yarjejeniyar da shugaba Xi Jinping da shugaba Zuma suka cimma daidaito a kai, da kuma sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da kungiyar AU da kuma dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka yadda ya kamata.
A nata bangare, Madam Zuma ta nuna godiya ga shugaba Xi Jinping bisa ga shawarwarin da ya bayar a taron koli na Johannesburg. Ta kuma marabci Zhang Ming a taron kungiyar AU. Zuma ta yabawa kasar Sin a kokarin da take na raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka da kungiyar AU, kungiyar AU tana son hada kai tare da kasar Sin don zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin jiragen kasa da na sama, hanyoyin mota, masana'antu, aikin gona, da kuma kiyaye tsaro, ta yadda za su samu moriyar juna da bunkasuwa tare. (Zainab)