Mr Ikounga, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai wanda aka gudanar, karkashin zama na 26 na kungiyar ta AU dake gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha.
Kwamishinan ya kuma jinjinawa muhawara ta biyar dake gudana, domin dunkule tunanin masu ruwa da tsaki game da ci gaban nahiyar, wadda ta samu halartar wakilai sama da 200, ciki hadda matasa, da wakilan kasashe, da ministoci tare kuma da shuwagabannin cibiyoyi daban daban.
Taron mahawarar wanda aka bude a ranar Laraba, na da nufin bada dama ta musayar ra'ayoyi tsakanin matasa da bangaren mahukunta, ta yadda za a kara karfafa hadin gwiwa, da fahimtar juna domin wanzar da ci gaba.(Saminu Alhassan)