A yayin ranar 'yan gudun hijira ta duniya, mamban hukumar siyasa ta kungiyar PLF Abbas Jumobi ya sanar da cewa, ikon dawowa na 'yan gudun hijiran Falesdinu ya kasance wani mataki mai tsarki, bai kamata a kwace ikon din daga hannayensu ba. Ya zuwa yanzu, ba a warware matsalolin Falesdinu yadda ya kamata ba, ciki hada da matsalar ikon dawowa na 'yan gudun hijira, kana ba a gudanar da kudurorin MDD dangane da batun Falesdinu yadda ya kamata ba, haka kuma, wasu kasashen duniya sun nuna bambanci a yayin da ake kan batun 'yan gudun hijiran Falesdinu.
Haka kuma, Abbas Jumobi ya kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su dauki nauyinsu yadda ya kamata kan batun Falesdinu, bai kamata su watsi da ikon dawowa na 'yan gudun hijiran Falesdinu ba, kuma ta tilasta wa Isra'ila wajen gudanar da kudurorin MDD da abin ya shafa yadda ya kamata. (Maryam)