Hukumar WHO ta bayyana cewa, matakan da aka dauka sun cimma nasarar hana karuwar yawan mutanen da suka kamu da cutar, don haka burin shirin tinkarar cutar na shekarar 2015 ya hada da hana yaduwar ta a kasashe masu fama da ita, har ma a sauran kasashe da yankuna a duniya, da kuma inganta hidimar badaaikin jinya don kara karfin tinkarar cutar da dai sauransu.
Bisa kididdigar alkaluman da hukumar WHO ta gabatar a wannan rana, an ce, yawan mutanen da aka zargi yi shakkar cewa su kamu da cutar Ebola ko kuma tabbatar da sun kamukamuwarsu da cutar ta Ebola a kasashen Guinea, Liberia da Saliyo ya kai 26,277, yayin da mutane wasu 10,884 a cikinsu suka mutu. (Zainab)