Matshidiso ta ce shirin hukumar WHO na shekarar bana, wanda ke maida hankali ga kare lafiyar mata, yara kanana, da sauran al'umma, zai yi matukar tasiri wajen dakile mace-mace dake da nasaba da cututtukan da ake iya kaucewa.
A cewar ta wannan manufa ta kunshi mai da kiwon lafiya a matsayin ginshikin inganta burin kare rayukan al'umma nan da shekarar 2030. A daya hannun tsarin na da burin ganin an kara yawan kudaden da ake warewa harkokin kiwon lafiya ga kowa da kowa.
Matshidiso ta ce tuni kasashe kamar Ghana da Rwanda, suka fara daukar matakan rage gibin dake tsakanin al'ummun kasashen su a fannin na kiwon lafiya, ta hanyar kafa tsare-tsaren inshorar lafiya. (Saminu)