Rahoton ya jaddada cewa, ba a ba da kariya ga dukkan mutanen da suke yin amfani da hanyoyin motoci yadda ya kamata, kuma akwai gagarumin gibi a tsakanin kasashe masu karfin tattalin arziki da kasashe masu tasowa. Ana samun mutuwar mutane a sakamakon hadarin mota da kashi 90 cikin dari a kasashe matalauta da masu tasowa, inda ake iya samun motoci da yawansu ya kai kusan kashi 54 cikin 100 na duniya kawai.
An ce, mutane masu tuka babura dake mutuwa a kan hanyoyin mota ya kai kashi 23 cikin 100, kuma wannan matsalar na cigaba da tsananta. Sannan mutanen dake yin tafiya da kafa da kuma kekuna su ne mutanen da ba su samun kariya a kan hanyoyin moto. (Zainab)