Jami'in na WHO wanda ya bayyana wannan hasashe yayin ganawar sa da manema labarai, ya kara da cewa tsare-tsaren inganta kiwon lafiya, da na bincike da sanya ido game da yaduwar cutar da ake gudanarwa sun yi tasiri matuka. Ya ce yanzu an kai ga matsayin bincikar ragowar wadanda ake zaton sun yi mu'ammala da masu dauke da cutar, maimakon matakin baya na kokarin bincikar wasu daga wadanda suka yi mu'ammala da masu dauke da cutar.
A daya hannun kuma Mr. Aylward ya yi gargadin cewa kalubalen da ake ci gaba da fuskanta, shi ne na tsammanin cimma nasara ba tare da daukar hakikanin matakai ba, musamman ganin yadda ake samun rahotanni na saba ka'idodjin kiwon lafiya yayin binne wadanda Ebola ta hallaka, da kuma gaza tantance mutane yadda ya kamata a yankunan da ake ci gaba da samun masu dauke da cutar.
Bugu da kari jami'in ya bayyana matsalar gudanarwa, da ta sufuri a yankuna masu wahalar shiga musamman ma a wannan lokaci na damuna, da kuma karancin kudade, a matsayin manyan kalubale da yaki da cutar Ebola ke fuskanta.(Saminu Alhassan)