Wang Yi ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin ganawar sa da 'yan jaridu a birnin Vienna. Ya ce ko da yake ana fuskantar matsaloli da dama, duk da haka ministocin harkokin wajen kasa da kasa sun yi namijin kokari na shiga-tsakani, inda a yanzu ake fatan nazari, tare da gabatar da jerin shirye-shiryen warware matsalolin da ake fuskanta, matakin da zai aza tubali na kammala shawarwarin karshe.
Mr. Kerry ya kara da cewa hakan babban ci gaba ne da aka samu, a yayin ganawar da ta wakana, tsakanin ministocin harkokin wajen kasashe masu fada-a-ji game da Nukiliyar Iran din a 'yan kwanakin nan.
Har wa yau Wang Yi ya bayyana cewa, mahalarta shawarwarin za su tattauna bisa wannan tushe. Yana kuma fatan za a kiyaye shawarwarin, da cimma daidaito cikin hanzari. Kana za a cimma yarjejeniya kan batun nukiliyar Iran cikin adalci da daidaito.
A hannu guda kasar Sin na yin takatsantsan wajen sa ran ganin cimma kyakkyawar makoma game da wannan batu. (Zainab)