Mr. Wang ya bayyana hakan ne ga 'yan jaridu, bayan kammalar taron ministocin Sin da na kasashen kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya(ASEAN) a jiya Laraba. Ya ce muhimmin fannin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen kungiyar ASEAN, yayin da suke yin kokarin raya hanyar siliki ta ruwa shi ne gina ababen more rayuwa, da hadin gwiwa wajen samar da kayayyaki. Ya ce Sin da kasashen kungiyar ta ASEAN na kan matakai daban daban a fannin bukasar masana'antu, wanda hakan ke ba su damar taimakawa juna.
Sai dai duk da hakan alamar hadin gwiwar dake tsakanin sassan ita ce la'akari da bukatun juna, da samar da ababen more rayuwa, da kayayyaki domin biyan bukatun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma, aikin da ke da matukar ma'ana.
Haka zalika Wang Yi ya bayyana cewa, yayin da Sin ke gudanar da hadin gwiwa tare da kasashen duniya, ba ta fatan hana sauran kasashen samun ci gaba, duk da yadda wasu kasashen ke fatan yin takara da kasar ta Sin a maimakon hadin gwiwa da ita. Don haka ya ce kamata ya yi kasashen duniya su yi amfani da fifikonsu domin gudanar da harkokinsu yadda ya kamata. (Zainab)