in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi shawarwari da ministan harkokin waje da raya yankunan Ghana
2015-07-17 10:04:03 cri

A jiya Alhamis ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da ministan harkokin waje da raya yankuna bai daya na kasar Ghana Hannah Tetteh a nan birnin Beijing.

A yayin shawarwarin, Wang Yi ya nuna yabo ga dangantakar sada zumunta da hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da Ghana, yana kuma fatan kasashen biyu za su ci gajiyar cika shekaru 55 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, da kara yin hadin gwiwa a fannonin sana'o'i, ayyukan more rayuwa, makamashi, sufurin jiragen sama, aikin gona, kamun kifi, alkarkatun kwadago, kiyaye tsaro da dai sauransu bisa tushen kara yin imani da juna a fannin siyasa, kana su yi kokarin kirkiro kyakkyawar makoma kan dangantakar dake tsakaninsu.

Wang Yi ya jaddada cewa, Sin ta nuna sahihanci ga hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka, kuma tana girmama tare da kiyaye moriyar kasashen Afirka da jama'arsu.

An inganta hadin gwiwar Sin da Afirka daga cinikin kayayyaki zuwa hadin gwiwa da zuba jari, daga daddale kwangila da gudanar da ayyuka zuwa hadin gwiwar gudanar da ayyyuka, daga yin mu'amala zuwa yin hadin gwiwa a manyan fannoni. Kamata ya yi bangarorin biyu su yi kokari tare don sa kaimi ga kyautata hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da bin sabuwar hanyar samun bunkasuwa tare.

A nasa bangare, Tetteh ya nuna godiya ga kasar Sin bisa ga taimakon da ta samar wa kasar Ghana don raya tattalin arzikinta, kuma ya amince da shawarar da Sin ta bayar game da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kana yana fatan za a kara yin shawarwari don inganta dangantakarsu. Hakazalika, Tetteh ya nuna yabo ga manufofin Sin da suka shafi kasashen Afirka, kana ya nuna godiya ga kasar Sin saboda kokarinta na taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da cutar Ebola. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China