in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar kasar Liberia ta gana da Wang Yi
2015-08-10 10:53:24 cri
A jiya ne shugabar kasar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf ta gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a birnin Monrovia, hedkwatar mulkin kasar Liberia.

A yayin ganawar, Wang Yi ya taya kasar Liberia murnar kawar da cutar Ebola a kasar, kana ya bayyana cewa, Sin tana son taimakawa kasar Liberia wajen sake gina kasar bisa bukatun kasar bayan da kasar ta samu nasarar kawar da cutar Ebola. Haka zalika, kasar Sin tana son taimakawa kasar a fannonin gina kayayyakin more rayuwa da horar da kwararru, da tsarin sha'anin kera kayayyaki da inganta karfinta na raya kasa da kanta.

A nata jawabin, shugaba Sirleaf ta bayyana godiya ga kasar Sin bisa ga gudummawar da ta baiwa kasarta a lokacin da cutar Ebola ta barke a kasar. Kana kasar Liberia tana son yin kokari tare da kasar Sin don raya kasar.

Bugu da kari, Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Liberia Augustine Kpehe Ngafuan a wannan rana a birnin Monrovia. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China