Rahotanni daga Najeriya suna cewa, a jiya kungiyar Boko Haram ta kai hari birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, inda suka halaka mutane 15.
Wasu bayanai na cewa, mayakan na Boko Haram sun sake kai wani hari a jiya da dare kan wani kauye da ke wajen birnin Maiduguri, inda wasu mata biyu 'yan kunar-bakin wake suka tada boma-bomai a cikin taron mutane, daga bisani kuma, suka bude wuta kan kauyawan. Bayan abkuwar lamarin, mazauna yankin sun bar gidajensu don tsirar da rayukansu.
Daga bisa ni sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da dakarun kungiyar Boko Haram, inda suka harbe 10 har lahira.(Lami)