Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane 17 ne suka gamu da ajalinsu kana wasu 41 suka jikkata a wani harin kunar bakin wake da aka kai a garin Madagali da ke jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa(ADSEMA) Haruna Furo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, wasu mata biyu ne 'yan kunar bakin wake suka kaddamar da harin ta hanyar tada bam din da ke jikinsu a cikin tashar motar garin na Madagali dake makwabtaka da garin Gwoza na jihar Borno.
Furo ya ce, an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin garin Mubi da kuma asibitin kwararru da ke garin Yola, fadar mulkin jihar Adamawa.
Shi ma kwamandan birget ta 28 da ke garin Mubi, Birgediya-Janar Victor Ezugwu ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai yi wani karin haske game da adadin wadanda suka jikkata ba. Amma ya bayyana cewa, al'amura sun daidaita kana an tsaurara matakan tsaro a garin na Madagali.
Don haka, ya bukaci jama'a da su rika sa-ido kan mutanen da ba su amince da take-takensu ba.
Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, mutane da dama sun rasa rayukansu baya ga wadanda suka jikkata a harin kunar bakin waken na ranar Litinin.(Ibrahim)