Kasar Sin ta bayyana bakin ciki kwarai da gaske dangane da mutuwa da jikkata musulmai da dama bayan da wani karfen daukan kaya ya fado ranar Jumma'a a babban masallacin harami da ke Mekka a kasar Saudiya.
Kakakin ma'aikatan harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai yau a nan birnin Beijing.
Hong Lei ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta yi bakin ciki kwarai da gaske dangane da hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar musulmai da dama, ta kuma mika ta'aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hadarin, tare da nuna jaje ga iyalan mamatan da kuma mutanen da suka jikkata sakamakon hadarin.
A baya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin da kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi sun mika sakon jaje daya bayan daya ga sarki Salman bin Abdulazizi Al Saud da kuma ministan harkokin wajen kasar Saudiya Adel al-Jubeir. (Tasallah Yuan)