A cikin wata wasika da aka fitar a wannan rana, Ayotalla Khamenei ya bukaci shugaban kasar ta Iran Hassan Rouhani da tawagar tattaunawar shi da su sa ido sosai dangane da yadda za'a aiwatar da yarjejeniyar ta nukiliya saboda Amurka ba kasar da zasu amince da ita ba ne.
Wannan ne karo na farko da Khamenei ya fito fili ya yi tsokaci a kan yarjejeniyar nukilyar da ake ta takaddama a kai wanda kuma aka cimma a yanzu tsakanin kasar ta Iran da sauran kasashe 6 da batun ya shafa wato kasashen din din din a MDD guda biyar da kuma Jamus a watan Yuli.
A cikin shekaru 8 wanda zai daidaita batun nukiliyar ta kasar Iran, kowane irin takunkumi a kowane mataki kuma a karkashin kowane suna, da zai hada da fakewa da kare hakkin dan adam da ta'addanci daga kowane kasa, da zai shafi batun tattaunawar nukiliyar da Iran, zai kasance saba wa yarjejeniyar inji wasikar.
Idan har wani bangaren yayi irin wannan yunkuri, gwamnatin Iran zata dauki matakin maida martani kuma zata dakatar da aiwatar da yarjejeniyar, inji wasikar har ila yau.(Fatimah Jibril)