Bayan ganawa da wasu jami'an kasar Saudiya, mista Blinken ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, kasar Saudiya ta dauki matakan soja kan dakarun kungiyar al-Huthiyyun tare da goyon bayan wasu kasashe, domin nuna musu cewa, ba za a iya hambarar da wata gwamnatin kasa mai ci ba ta hanyar karfin tuwo.
Ya kuma kara da cewa, kasar Amurka na gaggauta tura makamai zuwa kasar Saudiya domin nuna mata goyon baya, haka kuma, za su yi musayar bayanai da kuma kafa wani shiri cikin hadin gwiwa game da wannan lamari.
Bugu da kari, ya ce, kasar Amurka na ganin cewa, a halin yanzu, ya zama wajibi ta karfafa hadin gwiwarta da kasar Saudiya, har ma duk kasashen mashigin teku, domin sa kaimi ga kasar Yemen, musamman ma ga kungiyar al-Huthiyyun da magoyon bayanta da su bi yarjejeniyar siyasa da aka kulla a baya. (Maryam)