A ran 11 ga wata, wani karfen daukan kaya mai girma ya fado ba zato ba tsammani a masallacin Harami, wanda ya haddasa rasuwar mutane 107, yayin da sama da 200 suka jikkata, haka kuma, galibin dake cikin wadanda suka rasa rayukansu, su ne musulman da suka zo daga kasashen Indonesia da kuma India.
A halin yanzu, bangarorin da abin ya shafa na kasar Saudi Arabiyya sun fara gyara wurin da hadarin ya auku, da kuma fara gyara masallacin a wuraren da suka lalace sakamakon hadarin, domin sake karbar masu aikin hajji da sauri. Kana, hukumar addini ta kasar Saudi Arabiyya ta bayyana cewa, za a ci gaba da gudanar da ayyukan hajji na shekarar bana bisa lokacin da aka tsara, watau a ran 21 ga watan da muke ciki. (Maryam)