in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban kasar Sin ya halarci bikin nuna juyayi ga tsohon sarkin Saudiya marigayi Abdullah Bin Abd al-Aziz
2015-01-25 17:07:39 cri

Ranar Asabar 24 ga wata bisa agogon birnin Riyadh, hedkwatar kasar Saudiya, Yang Jiechi, manzon musamman na shugaban kasar Sin kuma mamban majalisar gudanarwar kasar Sin ya halarci bikin nuna juyayi ga tsohon sarkin Saudiya marigayi Abdullah Bin Abd al-Aziz, tare da ganawa tare da sabon sarkin kasar Salman bin Abdulaziz Al Saud.

A madadin shugabannin kasar Sin, gwamnatin kasar da kuma jama'ar kasar, mista Yang Jiechi ya nuna juyayi game da rasuwar marigayi Abdullah Bin Abd al-Aziz, ya kuma isar wa sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud da sakon shugaba Xi Jinping na kasar Sin, inda shugaba Xi ya ce, marigayi Abdullah Bin Abd al-Aziz, dan siyasa ne mai hangen nesa da kuma aka nuna ma girmamawa sosai. Ya ba da babbar gudummowa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da zaman karko da bunkasuwar tattalin arziki a Saudiya, da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa da kasa da shiyya-shiyya. Shugaba Xi ya yi bakin ciki sosai sakamakon rasuwar irin wannan abokin arzikin kasar Sin.

Har wa yau a cikin sakonsa, shugaba Xi ya sake taya wa sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud murnar zama sabon sarkin Saudiya, ya yi fatan cewa, a karkashin shugabancin sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, Saudiya za ta kara samun ci-gaba, za ta ci gaba da taka rawa a al'amuran kasa da kasa da shiyya-shiyya. Shugaba Xi ya bayyana fatansa na ci gaba da yin tattaunawa da sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud dangane da yadda za a inganta hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2 bisa manyan tsare-tsare, a kokarin raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa sabon mataki.

a nasa bangaren, sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud ya nuna godiya ga shugaba Xi Jinping na kasar Sin saboda ya aika da manzon musamman da ya halarci bikin nuna juyayin. Kasarsa ta Saudiya na son rika zurfafa hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasar Sin. Tana kuma maraba da ziyarar shugaba Xi cikin sauri.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China