Babban Magatakardan MDD Mista Ban Ki-Moon ta bakin kakakinsa ya sanar a ranar alhamis din nan, cewa yayi farin ciki game da farfadowar shawarwari a siyasance tsakanin bangarori daban-daban na kasar Burundi, inda kuma ya kalubalanci bangarorin da su shiga wannan aiki don warware rikicin siyasa a kasar.
Mista Ban ya yi kira ga shugabannin Burundi da su mai da hankali kan zaman lafiya da samun sulhuntawa tsakanin al'umma a maimakon moriyar jami'yyunsu, a cewarsa, hanya daya kawai ya kamata bangarori daban-daban su bi ita ce tattaunawa a siyasance cikin aminci tsakaninsu.
Haka kuma, Mista Ban ya nuna gamsuwa da goyon baya da kwamitin AU ke nunawa gwamnati da jama'ar Burundi,tare da fatan bangarorin zasu yi iyakacin kokarin warware rikicin kasar da samar da wata hanya a siyasance.
Idan ba a manta ba, an yi shawarwarin a ranar litinin din wannan makon a birnin Endebbe dake da nisan kilomita 40 kudu da Kampala babban birnin kasar Uganda, inda shugaban kasar kuma mai shiga tsakanin rikici Yoweri Museveni ya jagorancin taron. (Amina)