AU ta jaddada kiranta na ganin an tabbatar da zaman lafiya a kasar Burundi
Kungiyar tarayyar Afrika AU ta sake jaddada a ranar Talata da kiranta zuwa ga dukkannin bangarori daban daban na kasar Burundi, da su ba da hadin kai yadda ya kamata tare da tawagar zaman lafiya domin cimma wata hanyar lumana ga rikicin da kasar take fama da shi a halin yanzu. Madam Nkosazana Dlamini Zuma, shugaban kwamitin tarayyar AU, ta nuna yabo sake maido da tattaunawar neman zaman lafiya tsakanin 'yan kasar Burundu da aka bude a birnin Entebbe na kasar Uganda. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku