A cewar Jean Bosco Girukwishaka, wani jami'in mai kula da unguwar al'umma ta Muha na kasar, da misalin karfe 8 na daren Asabar ne maharan suka yi shiga irin ta jami'an 'yan sanda, suka yi dirar mikiya a mashayar waddda aka fi sani da Au Coin des Amis, sannan suka umarci ma'aikacin dake tattara kudade a mashayar da sauran mashayan da su mika musu kudaden da sauran kayyaki masu dajara da suka mallaka.
A cewar Girukwishaka, maharan sun umarci dukkan mashayan da su kwanta a kasa sannan daga bisani suka bude musu wuta inda nan take suka hallaka mutane 7 yayin da na 8 ya cika bayan kai shi aibiti.
Ya kara da cewa, wani mutum guda ma ya jikkata, kuma mutane 2 ne kachal suka tsira a yayin harin.
Girukwishaka ya kara da cewa, mashayar na kusa da wani barikin 'yan sanda ne, kuma an gano harin ne kwana guda da afkuwar lamarin, sannan maharani sun sace motar daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su.( Ahmad Fagam)