Binciken na farko shi ne an samu tashen tashen hankali na keta hakkin dan adam a kasar Burundi musammun ma kisa, tsare mutane ba bisa doka ba kuma dalilin rashin doka da oda, da kuma rashin hukunta masu aikata laifin, in ji madam Pancy Makula, shugabar wannan kwamiti a gaban manema labarai bayan wata tattaunawa tare da Gaston Sindimwo, mataimakin shugaban kasar Burundi na farko.
Madam Makula ta kuma bukaci gwamnatin Burundi da ta yi iyakacin kokarinta domin maido da zaman lafiya a cikin wannan kasa musammun ma a Bujumbura, babban birnin kasar. (Maman Ada)