A yayin fara wata mahawara da majalisar ta gudanar na tsawon sa'o'i 3, shugaban majalisar dokokin Pascal Nyabenda, ya ce batun tura dakarun samar da zaman lafiya ma bai taso ba, saboda kasar wacce ke shiyyar gabashin Afrika bata fuskantar matsalar da ta shafi kisan kiyashi.
Ya ce majalisar dokokin ta tabbatar da cewar, an fara samun kashe kashen rayuka ne a kasar daga watan Aprilu, a lokacin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya ayyana aniyar sa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku, lamarin da ya haifar da barkewar bore a fadin kasar.
Haka zalika, mafi yawan 'yan majalisar dokokin kasar sun bayyana cewar babu matsalar kisan kiyashi a kasar. Shugaban majalisar dattijan kasar Reverien Ndikuriyo ya bambance tsakanin kashe kashe da kuma kisan kiyashi.
'Yan majisar sun bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta daukar matakan kawo karshen matsalar aikata muggan laifuka a kasar don kaucewa duk wani yunkuri na kawo dauki daga kasashen ketare.(Ahmad Fagam)