Tsohon shugaban kasar Burundi Domitien Ndayizeye ya ce, muddin ana son lalubo bakin zaren warware rikicin da ya addabi kasar, sai an mutunta yarjejeniyar zaman lafiya ta Arusha, da ta kawo karshen bakin basasa na kasar daga shekarar 1993 zuwa ta 2005.
Ndayizeye, wanda ya shugabanci kasar tsakanin shekarar 2003 zuwa 2005, ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin na Xinhua a wata hira da ya yi kwanan nan cewar, yarjejeniya ta Arusha ta zayyana dukkanin hanyoyin da idan aka bi su, za a samu dawwamamen zaman lafiya a kasar Burundi.
Ya ce an tsara makomar Burundi a cikin wannan yarjejeniya. Kuma an tsara dokoki, wadanda da zarar aka aiwatar da su, za'a samu nasarar waraware tashin hankalin dake addabar kasar a halin yanzu.
Ndayizeye ya kuma kara da cewa, a lokacin tattaunawar cimma daidaito don kawo karshen yakin basasa na shekarar 2005, duk wasu bayanai dake da nasaba da matakan da za su kawo karshen rikicin na Burundi yana nan kushe a cikin yarjejeniyar.
Ita dai wannan yarjejeniya ta bi diddigin musabbabin rikicin kasar Burundi tun daga lokacin turawa 'yan mulkin mallaka, da kuma bayan mulkin mallakar.
Ndayizeye, ya ce rikicin kasar na baya bayan nan ya zo ne yayin da shugaban kasar mai ci Nkurunziza, ya nemi zarcewa a mulki karo na 3, wanda hakan ya ci karo da dokokin tsarin mulkin kasar.(Ahmad Fagam)