Kwamitin ya bayyana cewa, yana damuwa matuka kan rikicin siyasa da munanan sakamakon dake faruwa kan al'ummomin wannan kasa a halin yanzu.
Tare da yin allawadai da duk wani nau'in tashin hankali da rashin hukunta masu aikata laifi, da kuma kiraye kirayen rura wutar gaba da shugabannin siyasar Burundi suke yi, kwamitin sulhu ya yi kuma allawadai da hare haren da aka kaiwa sansanonin soja a Bujumbura, babban birnin kasar Burundi, da kuma a yankin karkarar birnin Bujumbura, haka kuma kisan mutanen da aka yi bayan wadannan hare hare.
Kasar Burundi ta fada cikin tashin hankali, tun lokacin da shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar a cikin watan Afrilun da ya gabata, niyyarsa ta neman wani wa'adin mulki na uku, lamarin da kuma 'yan adawa suka ce ya sabawa tsarin mulkin kasar.
Gwamnatin Burundi ta ki amince da matakin kungiyar Tarayyar Afrika na tura sojojin wanzar da zaman lafiya dubu biyar a kasar domin taimakawa wajen kawo karshen wadannan tashe-tashen hankali, inda gwamnatin ta bayyana cewa, za ta hana duk wasu sojojin wasu kasashe ratsa iyakokinta, a cewar wasu kafofin watsa labaru. (Maman Ada)