Shugaban hukumar Jean Baptiste Baribonekeza shi ne ya bayyana hakan,bayan wasu hare-haren da aka kai kan barikokin soja da ke ciki da wajen birnin Bujunbura,fadar mulkin kasar.
Ya kuma yi kiran da a kara samar da tsaro a kasar, sannan jama'a su kasance masu mutunta 'yancin bil-adama
Kakakin rundunar sojan kasar Kanar Gaspard Baratuza, ya shaidawa manema labarai cewa, hare-haren na ranar Jumma'a sun sabbaba mutuwar a kalla mutane 87, ciki har da 'yan bindiga 79 da sojoji guda 4 da kuma 'yan sanda 4, kana sojoji 9 da 'yan sanda 12 sun jikkata.
Baratuza ya kara da cewa, an kama mahara 45, kana sojojin sun yi nasara kwace bindigogi daban-daban guda 97 da kuma albarusai.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ne dai wasu 'yan bindiga suka kai hare-hare a jere kan barikokin soja guda uku dake Bujungura, fadar mulkin kasar ta Burundi da kuma daya da ke Mujejuru a wajen lardin Bujunbura, hare-haren da hukumar ta CNIDH ta yi Allah-wadai da shi.(Ibrahim)