A safiyar ranar 11 ga wata, dakaru sama da 150 sun kai hari kan sansanonin soja dake birnin Bujumbura, hedkwatar kasar Burundi, ciki har da babban kwalejin aikin soja a Musaga dake birnin Bujumbura, da wani sansanin soja dake Ngagara. Kakakin rundunar sojan Burundi Gaspard Baratuza ya bayyana cewa, a cikin wannan hari, dakaru 79 sun mutu, yayin da aka cafke mutane 45, da karbe bindigogi 97 da harsashi da yawa. A sa'i daya, sojoji 4 da 'yan sanda 4 sun rasu sakamakon hakan, yayin da sojoji 9 da 'yan sanda 12 suka jikkata.
Ban da haka, an ba da labarin cewa, a jiya Asabar an tarar da gawawwakin fararen hula 40 a birnin Bujumbura. Wani jami'in wurin ya bayyana cewa, wadannan fararen hula sun mutu ne sakamakon musayar wuta daga sassafe zuwa dare na ranar 11 ga wata.(Fatima)