Kungiyar a cikin sanarwar da ta fitar a jiya Jumm'a ta jaddada kiranta ga gwamnatin kasar Burundi da a cikin gaggawa ta amince da sake daukan tawagar shirin ayyukan ba da kariya da tsaro na Afrika da aka fi sani da MAPROBU.
Shugaban kwamitin kungiyar ta AU madam Nkosazana Dlamini-Zuma tana ci gaba da sa ido kwarai game da yanayin da ake ciki a Burundi da nufin samar da mafita na zaman lafiya a cikin hanzari a kan halin rikicin da ake ciki a yanzu, in ji sanarwar.
Tana kuma kira ga daukacin masu fada a ji na kasar da su ba da cikakken goyon bayan su ga tattaunawar su kuma dora abin da zai amfana ma kasar a kan gaba da komai.
Shugaban ta AU Madam Zuma daga nan sai ta jaddada cewa dole sai tattaunawa na hakika da kuma zai kunshi ainihin kowa a cikin shi ne kawai zai saka masu ruwa da tsaki na kasar su shawo kan kalubalolin da ake fuskanta a yanzu. (Fatimah Jibril)