A cikin jawabin da ya gabatar a filin saukar jiragen saman kasar, mista Xi ya ce Sin da Zimbabwe kawayen juna ne, kuma dankon zumunci da shugaba Robert Mugabe da tsoffin shugabannin Sin suka kulla, ya haifar da karuwar arzikin kasashen biyu.
Tun kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu tsawon shekaru 35 da suka shude, bangarorin biyu na baiwa juna taimako da boyon baya, tare da cin moriyar juna, da dogaro da juna, baya ga ci gaba mai armashi a fannoni daban-daban da suka samu, ciki hadda fannin siyasa, da tattalin arziki da ciniki, da musayar al'adu da dai sauransu. (Amina)