in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi da Putin sun cimma ra'ayin karfafa hadin gwiwa ta fuskar yaki da ta'addanci
2015-12-01 10:40:10 cri

Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi jinping tare da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun cimma matsaya guda a birnin Paris domin karfafa hadin gwiwa ta fuskar yaki da ta'addanci.

A yayin wata ganawa tare da mista Putin yayin babban taron MDD kan sauyin yanayi, mista Xi ya bayyana cewa, bisa la'akari da sauye sauyen da suka faru sosai a bangaren yaki da ta'addanci a duniya, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da gamayyar kasa da kasa, har ma da kasar Rasha, domin yaki da ta'addanci da kare moriya guda ta kasashen duniya.

Dangantakar game da manyan batutuwa na kasar Sin da na Rasha na samun ci gaba da zurfafa, in ji shugaban kasar Sin, inda ya kara da cewa, fadada yin musanya a matsayin koli na da muhimmanci sosai. Kasar Sin a shirye take wajen kara rubanya kokarin hadin gwiwa tare da Rasha domin kara ingiza huldar danganataka a fannoni daban daban, in ji shugaba Xi Jinping.

A nasa bangare, mista Putin ya bayyana cewa, duniya ta fuskanci sauye sauye masu sarkakiya da zurfi, kuma Rasha na fatan yin aiki tare da kasar Sin wajen karfafa dangantaka a fannoni da dama, kamar yaki da ta'addanci, da kuma bunkasa demokuradiya a cikin tsarin dangantakar kasa da kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China